Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa, bata da ikon tilasta jami’o’i su tafi hutu Dan bawa Dalibai damar yin jefa kuri’a a zabe mai zuwa.

Mai taimakawa Shugaban hukumar a bangaren kafofin sadarwa Rotimi Oyekenmi, shi ya bayyana haka a zantawarsa da jaridar Punch a yau Asabar.
Hakan ya biyo bayan kiraye-kiraye daga mabanbantan jama’a Na cewa yakamata jami’o’in su bayar da hutu, Dan Dalibai su samu damar karbar Latin zabe da kuma yin zaben mai gabatowa.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai wani Dan Majalisa a majalissar wakilai ta kasa Kabiru Tukura, ya shigar da kudurin gaggawa na bukatar a bawa Daliban manyan makarantu damar yin zabe.

Tukura ya bayyana cewa, Shugaban INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya fadi cewa, adadin Dalibai Miliyan uku da dubu Dari takwas ne suka yi sabuwar rajistar zabe.
A lokacin da INEC ita kuma ta fadi cewa bata da hurumin tilastawa jami’o’in bayar da hutu dan zabe, wannan hurumi ne na shugabannin gudanar da kowacce Jami’a.
Lokacin da aka tuntubi shugaban kungiyar shugabannin jami’o’in Farfesa Samuel Edoumiekumo yace, da majalissar wakilai da hukumar kula da Jami’o’in ta kasa. Babu wanda yake da ikon tursasawa manyan makarantun tafiya hutu.