A yau Laraba, kotun kolin Najeriya ta dakatar da yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na hana amfani da tsaffin takardun Naira.

Kwamitin Alkalan kotun guda bakwai karkashin jagoranicin Justice John Okoro, ya dakatar da shirin bisa karar da wasu gwamnonin Arewa uku suka shigar.

Gwamnonin sun hada da Nasir El-Rufa’i na Kaduna, Muhammad Bello Matawalle na Zamfara, da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi.

Gwamnonin uku sun bukaci kotun ta dakatar da shirin hana amfani da tsaffin takardun Naira da gwamnatin tarayya da babban bankin tarayya CBN ke kokarin yi a ranar 10 ga Febrairu, 2023.

Lauyan masu kara, Mr A. I Mustapha, SAN, ya bukaci kotun ta amince da bukatarsu saboda jin dadin al’ummar Najeriya.

Ya bayyana cewa wannan doka ta gwamnati ta jefa yan Najeriya halin kakanikayi.

Ya kara da cewa yan Najeriyan da basu da asusun jaiya na banki sun kai kashi 60%, hakan bisa rahoton bankin CBN da kansa.

Lauyan ya kara da cewa muddin kotun koli bata shiga lamarin ba Najeriya na iya shiga wani irin hali saboda bankuna har sun fara rufe ofishohinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: