Hukumar zaɓemai zaman kanta a Najeriya INEC ta tabbatar da cewar za ta tabbatar jami’an tsaro sun bayarda kulawa da kariya ga masu buƙata ta musamman a yayin zaɓe.

Shugaban hukumar ne ya jaddada haka yau a taron ƙaddamar da wata gidauniya da aka shirya domin duba haƙƙin masu buƙata tare da ba su dama don shiga al’amuran zaɓe.

Wannan ke nuni da cewar masu buƙata ta musaman za su shiga tsarin aikin hukumar zaɓe na wucin gadi a babban zaɓen shekarar 2023.

Taron wanda ya samu halartar manyan jami’an tsaro da ƴan sanda wanda su ka bayarda tabbbacin bayar da kariya ga mutane masu buƙata ta musamman.

Taron wanda ya samu shugabanhukumar zaɓe na ƙasa ya samu wakilcin kwamishinan zaɓe na ƙasa shiyyar kudu maso yama Farfesa  Kunle Ajayi.

Ya ce hukumar za ta tabbatar tsarin da ta samar domin bai wa masu buƙata ta musamman dama da ƴanci ya yi aiki yadda ya kamata a babban zaɓen da ake tunkara.

Kwamishinan ƴan sanda mai kula da al’amuran zaɓe  Basil Idegwu ya tabbatar da cewar za a samar da isasun jami’an tsaron da za su kula da masu buƙata ta musamman a yayin babban zaɓen.

Cibiyar ta ƙaddamar da shirin ne don ganin yadda mutane ke fargaba a wajen zaɓe wanda hakan ke sa da dama daga cikin mutane ke ƙauracewa ayyukan taimakawa zaɓe musamman a ranar zaɓe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: