Akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar cutar sankarau a jihar jigawa a farkon shekarar 2023.

Kamar yadda rahoto daga hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar ta ce cutar sankarau ta hallaka mutane 18 a jihar jigawa wadda ke da iyaka da Damagaran ta kasar Niger.

Sai dai hukumomi a jihar ta jigawa sun ce sun yi taron gaggawa da masana musamman hukumar dakile cututtuka masu yaduwa wato NCDC kuma ta ce ba ɓata lokaci za ta fara rarraba riga-kafin wannan cutar ga yankunan jihar.

Sannan masana na bayyana cewa cutar sanƙarau cuta ce mai hadarin gaske wadda ke shafar matsalar kwakwalwa da Kuma Laka wadda har ya zuwa yanzu ke kalubalantar daniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: