Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa, bata da kudurin dage babban zaben shekarar nan ta 2023 wanda yake daf da karatowa.

Sashin hukumar a kafofin sadarwarta na zamani ya karyata wasu rahotanni da ake yadawa da bayyana su matsayin na bogi, rahotannin da suke bayyana cewa INEC zata iya daga zaben zuwa sati daya ko biyu.
INEC ta sanar da yan Najeriya da suyi watsi da labaran bogin da ake yadawa, tace zabe yana nan zai wakana kamar yadda aka tsara.

Sun ce an jawo hankalin su game da wasu labaran karya da ake bazawa a kafofin sadarwa na zamani dauke da batun za’a dage zaben mai zuwa.

Sun kuma ce hukumar ba zata yi kuma bata tunanin daga zaben mai gabatowa, Dan haka yan Najeriya su yi watsi da batun.
Hukumar shirya zaben ta sha fadin cewa, duk da kalubalen da kasar ke fuskan da kuma hukumar, zaben zai wakana kamar yadda aka tsara.