Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC reshen jihar Sokoto ta fara raba kayan aiki zuwa kananan hukumomin jihar a yau Alhamis.

Kana hukumar ta tabbatar da cewa ta shirya tsaf domin gudanar da sahihin zabe a ranar asabar mai zuwa kamar yadda ta tsara.
INEC ta bayyana hakane ta bakin shugaban ta na jihar Sokoto Dr. Nura Ali. a birnin Sokoto a safiyar yau Alhamis.

Dr. Nura Ali ya kara da cewa sun kammala tantancewa tare da bayar da horo ga dukkan ma’aikatan wucin gadi na fadin jihar.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Sokoto Dr. Nura Ali ya bayyana cewa suna da wadatattun kayan aiki harma da na jiran kota kwana domin tabbatuwar zaben a ranar asabar kamar yadda hukumar ta lashi takobi.