Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa, wasu ‘yan daba sun yi awon gaba da na’urar tantance masu kada kuri’u ta BVAS da jihohin Katsina da Delta.

Mahmud Yakubu, shugaban INEC ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Abuja kan halin da ake ciki a zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya.


Yakubu ya shaida cewa, duba da yadda zaben ke gudana a kasar, alamu sun nuna akwai kalubalen da ba a rasa ba.
Ya ce, kalubalen da ake fuskanta sun hada da matsalar jigilar kayan aikin zaben da kuma rashin tsaro.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, tuni hukumar ta zabe ta tabbatar da maye gurbin na’urorin da aka sacen don ci gaba da zabe a yankunan.
A cewar shugaban na INEC, an sace wasu na’urorin ne a karamar Safana ta jihar Katsina a Arewa maso Yammacin Najeriya.
A gefen Kudancin kasar nan kuwa, an sace na’urorin na BVAS ne a karamar hukumar Oshimili ta jihar Delta.
Da yake bayyana matakin da aka dauka, shugaban ya ce an maye gurbin na’urorin yayin da ‘yan sanda suka kwato uku daga cikin shida na na’urorin da aka sace a jihar Katsina.