Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta dakatar da kwamishinan zabe a jihar Sakkwato, Dakta Nura Ali, kuma matakin ya fara aiki nan take.

Hakan na ƙunshe ne a wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Sakataren INEC, Rose Orlaran-Anthony, da aka aikewa sakataren hukumar na jihar.
Wasiƙar ta umarci Dakta Ali ya tattara ya bar Ofishin hukumar INEC da ke jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya, har sai baba ta gani.

Haka nan INEC ta umarci Sakatariyar gudanarwa, Hajiya Aliyu Kangiwa, ta maye gurbinsa nan take.

Wannan na zuwa ne awanni 48 bayan shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya lashi takobin gano jami’an hukumar masu sakaci da ɗaukar mataki, sai ga shi ya cika kalamansa a aikace.
Duk da wasiƙar ba ta ambaci dalilin ɗaukar wanna mataki kan REC ɗin ba, amma wata majiya a INEC ta shaida wa Daily Trust cewa yana da alaƙa da abinda wasu ma’ikatan karkashin Ali suka yi a zaben da ya gabata.