Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta tabbatar da konewar waasu shaguna guda 14 daa rumfuna biyar a wata gobara da aka yi a kasuwar Rimi.

Mia magana da yawun hukumar Saminu Yusif ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Lamarin ya faru a yau Laraba da misalin ƙarfe 1:46 na rana.

Daga cikin gine-ginen da su ka ƙone har da masalli a kasuwar.

Sai dai bayan isar jami’ansu sun samu nasarar kashe gobarar tare da kubutar da sauran shagunan.

A gobarar daa ta faru ba a samu asarar rai ko rauni ba.

Tuni hukumar ta fara bincike domin gano dalilin faruwar gobarar.

Hukumar ta ja hankalin al’umma da su dinga kashe kayan lamtarki bayan kammlaa amfani da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: