Wasu da ake zargin Masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da mutane 50 bayan sun hallaka mutane biyar.

Al’amarin ya faru da yammacin ranar Talata abgarin Agwa da ke ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin mutane biyar da aka kashe har da wata mai juna biyu da take dauke da ciki wata shida.

Wani shaidar gani da ido mai suna Mallam Audu ya ce maharan sun shiga garin su na harbe-harbe lamarin da ya kai ga hallaka mutanen.

Da yawa daga cikin mutanen ƙauyen sun samu rauni yayin da su ke tserewa don kuɓutar da rayuwarsu.
Ya ce an yi garkuwa da mutane fiye da hamsin.
Sai dai ƴan bindigan sun yi musayar wuta wasu sojoji lamarin da ya sa su ka gudu zuwa cikin daji.
Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida a jihar Neja Emmanuel Umaar ya tabbatar da faaruwar laamarin.
Sai dai bai bayyana adadin mutanen da aka sace ba yayin da su ke ci gaba da tattara bayanai a kai.