Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Legas bayyana cewa, ta daga ranar da za’a koma harkokin karatu zuwa 21 ga watan Maris din da muke ciki.

Wani jawabi bisa sahalewar shugaban jami’ar farfesa Folasode Ogunsola, ya amince da dage komawa makarantar zuwa 21 ga watan Maris din Shekarar 2023.
Ya kuma kara da cewa dukkan wasu ayyuka kamar taruka zasu cigaba da wanzuwa kamar yadda aka tsara, amman banda daukar darussa.

Sanarwar ta kara da cewa dage komawa makarntar ya biyo bayan canja lokacin gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalissun jihohi da aka yi, daga ranar Asabar 11 ga watan Maris zuwa Asabar 18 ga watan Maris din.

An kuma bukaci wadanda suke zaune a cikin makarantar da su zauna cikin lafiya, tsaro da bin ka’ida, kuma su lura da faruwar komai ciki da waje.
Idan za’a iya tunawa dai gwamnatin tarayya ta bayar da umarni tun a baya cewa, dukkan daliban manyan makarantun kasar nan su koma gidajensu don gudanar da babban zaben shekara ta 2023.