Alamu na nuni da cewa, shugaban majalisar wakilai na tarayya Femi Gbajabiamila ya shiga daga yan gaba-gaba na wģaɗanda zasu iya zamtowa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa a mulkin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ba’a ga fuskar Gbajabiamila ba sam a wajen amsar takardar shaidar cin zaɓe ba, a lokacin da INEC ta rabawa waɗanda suka ci zaɓen takarar da suka tsaya shaidar su domin dawowa majalisa ta 10 ba.


An dai sake zaɓar Gbajabiamila ne domin ya wakilci mazaɓar sa ta Surulere 1 dake jihar Lagos ne, a wani salo na ya wakilce su karo na 6 a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Ya samu kuri’u 19,717 ne dai, yayin da abokin karawar sa na kusa kusa Bosun Jeje na PDP, yasha kaye ƙuri’u 5,121.
Qn rawaito cewa a ranar juma’a, shugaban na majalisar ka iya watsi da majalisa, domin ana kyautata zaton zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sahale bashi muƙamin shugaban ma’aikatan Aso Villa a gwamnatin sa.
Wata majiya mai tushe daga gidan su Gbajabiamila ne ta tabbatar da zargin.
Gbajabiamila ya kasance ɗan amanar Tinubu na gaba-gaba, kuma tunda yayi aiki da duk wani dan siyasa a matakin tarayya shekaru 20 da suka wuce zuwa yau, hakan yasa Tinubu ke kallon sa a matsayin wanda yafi dacewa da muƙamin.