Hukumar tsaron farar hula NSCDC ta ce ta kama mambobin wata tawaga da aka ce suna sarrafa tare da raba jabun dalolin Amurka da sabbin takardun naira.

Ya yin hirarsa da kamfanin dillancin labarai NAN ranar Juma’a a Abuja, Olusola Odumosu, jami’in hulda da al’umma na hukumar ya ce an kama wadanda ake zargin ne a jihar Filato tsakanin 22 ga watan Fabrairu zuwa 8 ga watan Maris.


Odumosu ya ce mambobin daya daga cikin tawagar, sun kunshi maza hudu, an kama su ne dauke da dallar Amurka na bogi dubu 64,800 da dub 475,000.
Ya kuma ce an kwato jabun kudi har naira miliyan 1.5 daga hannun tawagar ta biyu da ta kunshi maza biyar.
Ya kara da cewa an kama tawagar ta farko ne bayan samun bayanan sirri cewa suna kan hanyarsu na zuwa kai wa wani abokin harkarsu kudin jabu a jihar Nasarawa.
Odumosu ya kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa suna da hannu kan abin da ake zargin suna yi, yana mai cewa rundunar na zurfafa bincike kuma tana farautar sauran mambobin tawagar.