Jam’iyyar Labour ta zargi hukuman zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, da kawo cikas ga karar da ta shigar na kallubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023.

A wurin taron manema labarai a Legas, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar, Dr Yunusa Tanko, ya zargi INEC da saba umurnin kotun sauraron karar zaben shugaban kasa wacce ta bai wa jam’iyyar da dan takarar shugaban kasarta, Peter Obi, daman duba ainihin kayayyakin da aka yi amfani da su yayin zaben.

Ya ce an gabatarwa INEC takardar kotu a ranar 3 ga watan Maris duk da cewa hukumar ta samu wakilci a zaman kotun lokacin da aka bada umurnin.

Ya ce jam’iyyar ta kuma aika wasika ga hukumar zaben a ranar 6 ga watan Maris, tana tunatar da ita cewa ba ta riga ta bi umurnin kotun ba.

Yunusa ya yi barazanar cewa jam’iyyar Labour za ta umurci magoya bayanta su yi zanga-zangan lumana a dukkan ofisoshin INEC kan rashin bin umurnin kotun, yana mai cewa dole ne kowa ya bi umurnin kotu a karkashin dimokradiyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: