Daga Mustapha Gambo

Shugaban hukumar Nafdac A jihar Kano Ya bayyana cewar binciken gani da ido da hukumar ta gudanar ya tabbatar da cewar kwayoyin magani katon 303 da rundunar Yansandan Jihar Kano suka kama kwayoyin Diflofenac ne da ake amfani da su don wakar da cutar mura da kuma masu fama da cutar sanyi, shugaban hukumar NAFDAC a jihar Kano ya kara da cewa babu sinadarin da ke sanya a yi maye a cikin kwayar Diflofenac
Insert.
Shaba Muhd ya bayyana takaicinsa yadda kwamishinan Yansanda Wakili Muhammad ya bayyana cewar kwayar tramadol ce ya kama, a taron manema labarai, yace kamata yayi kwamishinan ya tuntubi masana daga hukumar NAFDAC ko NDLEA don yin gwaji akan kwayoyin kafin ya bayyanawa manema labarai.
Insert..
Shugaban hukumar NAFDAC a jihar Kano shaba muhd Ya yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki da su hada hannu wuri guda domin magance tuammali da miyagun kwayoyi a tsakanin alumar jihar Kano, cikin sauki.
Idan dai zaa iya tunawa a makon da ya gabata ne kwamishinan Yansandan jihar Kano Wakili muhd ya bayyana cewar katon 303 da ya kama kwayoyin Tramadol ne. Ko a baya bayan na ma sai da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta bayyana takaicinta yadda kwamishinan Yansanda ya yi ikirarin cewar kwayoyin Tramadol ya kama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: