Gwamnatocin Jihohin da suka kai gwamnatin tarayya kara akan kudirin sauya fasalin takardun kudi, sun bai wa ministan shari’ah Abubakar Malami SAN da gwamnan babban banki Godwin Emefiele zuwa ranar Talata, da su bi umarnin da kotun koli ta bayar.

Gwamnonin jihohin sunyi barazanar shigar da korafin raini ga kotu akan dukkan su biyun, idan har basu yi biyayya akan umarnin kotun na cigaba da karbar tsoffin takardun kudi na Naira 200, 500 da 1000 ba.

Sama da mako guda kenan tunda kotun kolin ta bayar da umarnin, Amman ministan shari’ar da gwamnan bankin sun yi shiru akan lamarin, wanda shirun da suka yi ya sanya ‘yan Najeriya suka ki cigaba da karbar tsoffin kudin a harkar kasuwancinsu.

Jaridar Punch a ranar Asabar ta ruwaito cewa ranar Juma’a an kaiwa gwamnatin tarayya da kwafin takardar umarnin kotun, Wanda ta ayyana tsoffin kudin a matsayin halastattu har nan da watanni goma.

Lauyan Jihohin Kaduna, Kogi da Zamfara wadanda suka kai gwamnatin tarayya kara zuwa kotun kolin Abdulhakeem Mustapha SAN ya bayyana cewa, an sanar da Malamin umarnin kotun kuma an bashi kwafin takardan hukuncin a ranar Juma’a da rana.

Ya kara da cewa suna kuma tsammanin zasu bi umarnin kotun ba tare da bata lokaci ba, sakamakon dukkan abinda ake bukata an bai wa gwamnatin da kuma bankin na CBN.

Leave a Reply

%d bloggers like this: