Wasu ‘yan bindiga sun bukaci a biya su sabon kudin fansa naira miliyan biyu da babura biyu domin su sako wata mata da diyarta da aka sace a unguwar Janjala da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

 

Ƴan bindigar a ranar 5 ga Fabrairu, 2023, sun kai hari gidan wadanda abin ya shafa suka tafi da matar mai suna Shamsiya da mijinta, Mustapha da ‘yarsu mai shekara 16, Mahapuza.

 

Sai dai bayan an biya Naira miliyan biyu kudin fansa, barayin sun sako Mustapha tare da tsare Shamsiya da Mahapuza.

 

Madaki na Janjala, Samaila Babangida, yayan Mustapha, ya shaida wa wakilin Daily Trust ta wayar tarho a yau Talata cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a kara biyan nakra miliyan biyu da babura biyu domin su sako sauran wadanda abin ya shafa.

 

A cewarsa, masu garkuwan sun saki Mustapha ne a ranar Litinin, bayan sun karbi Naira miliyan biyu, inda suka ce, sun sakeshi be Mustapha ya je ya tara Naira miliyan biyu da sabbin babura guda biyu kafin a sako matar da diyarta.

 

Babangida ya ce Mustapha a halin yanzu yana kwance a asibiti yana jinya sakamakon halin da ya samu kansa a hannun masu garkuwan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: