Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya bayyana cewa umarnin da babban bankin Najeriya (CBN) yabi kan halaccin tsaffin kuɗi, babbar nasara ce ga ƴan Najeriya.

 

Gwamnan ya ce yanzu al’umma sai su sanya ran su a inuwa domin ana tsammanin kuɗi za su wadatu a dalilin wannan umarnin na babban bankin.

 

Babban bankin Najeriya a ranar Litinin ya buƙaci bankuna da su riƙa bayar da tsaffin kuɗi sannan su karɓi tsaffin kuɗin na hannun mutane har zuwa 31 ga watan Disamba, kamar yadda kotun ƙoli tayi umarni.

 

A wata sanarwa da Zailani Bappa, mai bayar da shawara na musamman kan watsa labarai ga Matawalle, ya fitar, gwamnan yace ƙarar da wasu gwamnoni suka shigar kan sauya fasalin takardun kuɗi, domin amfanin masu ƙananan sana’o’i ne da ƴan Najeriya.

 

Ya ce waɗanda suka zarge su da zuwa kotu saboda zaɓen shugaban ƙasa duk da kukan da ƴan Najeriya ke yi kan sabon tsarin, yanzu sun ji kunya domin ba suyi ƙasa a guiwa ba har sai da suka samu nasarar buƙatar su na ganin an kawo ƙarshen sa.

 

Ya kara da cewa Dukkanin ƴan Najeriya yanzu hankulan su za su kwanta dangane da lamarin, sannan su na buƙatar kuɗaɗe su wadatu domin rage raɗaɗin da suke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: