Kungiyar kwadago a Najeriya ta umarci mambobinta da su yi dafifi a ofisoshin babban bankin kasa na CBN na jihohin kasar baki daya.

Shugaban kungiyar na kasa Joe Ajaero ne ya yi umarnin yayin ganawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce sun ɗauki matakin hakan ne domin ganin babban bankin ya wadata kasar da takardun kudi da su ka yi karanci.

Kungiyar ta yi taronta a ofishintaa da ke Abuja yau Laraba.

Tun tuni kotun koli a Najeriyaa ta yi umarni gaa babban bankin kasa da ya bayar da umarnin ci gaba da karbar takardun kudi na naira 200, 500 da kuma naira 1,000 da aka sauyawa fasali.
An kai ruwa rana bankin na jaddada haramta amfani da tsaffin takardun kudin.
Mutane na kokawa daangane da karancin sabbin takardun kudin da aka sauya.
Sai dai gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta yi hakan ne da mufin daƙile cin hanci da rashawa, ta’addanci da kuma toshe haanyoyin zirarewar kudi babu dalili.