Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa jami’an rundunar sun samu nasarar hallaka mayakan boko haram 48 yayin da 974 su ka mika wuya.

Daraktan yada labaran rundunar Manjo Janar Musa Danmadami ne ya tabbatar da hakan a yayin ganawa da manema labarai.
Dan madami ya bayyana cewa mayakan sun mika wuya ne a makonni biyu da su ka gabata ciki har da iyalansu.

Manjo Musa ya ce kafin samun nasarar rundunar tayi amfani da salo kala daban-daban akan mayakan na Boko Haram.

Kakakin ya kara da cewa dakarun rundunar na Operation hadin kai sun kaddamar da wasu hare-hare akan makayan na boko haram a ranar 23 ga watan Maris din da ya gabata a cikin kananan hukumomin Askirar Uba, Bama da kuma Mafa tare da hallaka bakwai daga cikin mayakan inda sauran su ka tsere.
Sannan jami’an sun samu nasarar kwato kayayyaki da makamai masu tarin yawa ciki harda kekuna da Babura, kayan hada bama-bamai da sauransu.
Kuma sun sake tarwatsa sansanin mayakan wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan mayakan da dama wasu kuma su ka jikkata.
Ya ce an kaddamar da hare-haren ne da jirgin yakin jami’an.