Gwamnan Jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya kafa kwamiti mai mutane 41 wanda zai yi aikin tsare-tsare domin mika mulki ga sabuwar gwamnatin Jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Jihar Kabiru Balarabe ya fitar a ranar Alhamis.

Balarabe ya bayyana cewa tsohon ministan kudi Bashir Yuguda ne zai jagoranci kwamitin.

Sauran sun hada da sakatare a kwamitin Dr Lawan Hussaini babban sakataren harkokin Majalisar zartarwa a ofishin gwamna mai ci da sauransu.

Kamfanin dillancin labaran Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa kwamitin zai yi aikin tabbatar da mika mulki ga sabuwar gwamnatin Jihar cikin tsari tare da samar da bayanan da su ka dace ga sabuwar gwamnatin.

Za dai a rantsar da sabbin shugabannin a Najeriya ciki harda shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, inda a Jihar ta Zamfara za a rantsar da Dauda Lawal a matsayin sabon gwamnan Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: