Fadar Shugaban Kasa ta ce a fannin tsaro da habaka tattalin arziki, Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Najeriya fiye da yadda ya same ta a 2015.

 

Kakakin shugaban, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels ranar Talata.

 

Ya kuma karyata zargin da ake yi na cewa a tsawon mulkin Buhari na shekara takwas, ya nuna kabilanci wajen nadin shugabannin hukumomin tsaro.

 

A cewarsa, nadin nasu ba shi da wata alaka da addini, yanki ko kabilar da mutum ya fito, an fi la’akari da cancanta tun da dai doka ta ba shugaban ikon nada duk wanda ya ga dama.

 

Dangane da zargin cewa an fi kashe mutane a mulkin Buhari a kan shekarun baya duk da cewa bangaren tsaro na cikin manyan abubuwan da ya yi alakawari a kansu, Femi Adesina, ya ce ba gaskiya ba ne.

 

Ya ce, ka san cewa akwai wani rahoto da ya ce an fi samun karancin kashe mutane a 2022 a cikin shekara 12 da suka gabata a sakamakon ayyukan ta’addanci? Sanin kowa ne a Najeriya cewa alkaluman sun ci gaba da sauka a tsawon shekaru.

 

Gaame da tattalin arziki kuwa, Femi Adeshina ya ce gwamnatin Buhari ta fadada hanyoyin samun kudaden shigar Najeriya, ta yadda a yanzu kasar ta rage dogaro kacokam da danyen man fetur.

Leave a Reply

%d bloggers like this: