Rahotanni daga jihar Nassarawa na nuni da cewar wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da direban matamakin gwamnan jihar.

An yi garkuwa da Daniel Ogoshi a gidan abokinsa da misalign ƙarfe 09:30pm na daren Talata.

Ƴan uwan Daniel sun tabbatar da cewar an yi garkuwa das shi ne a daren jiya.

Mataimakin gwamnan jihar Nassarawa Emmanuel Eyima ya tabbatar da haka, wanda yace ya samu labarin faruwar lamarin.

Ko a ɓangaren yan sanda sun tabbatar da yin garkuwa da direban mataimakin gwamnan, kamar yadda mai Magana da yawun ƴan sandan jihar Ramhan Nansel ya shaida.

Sai dai ya ce zai bayar da cikakken bayani ga ƴan jarida bayan tatara bayanai dangane da abin daya faru.

Har zuwa lokacin da mu ke kamala wannan labari maharani bas u tuntuɓi iyalan direban ko akwai abinda su ke buƙata kafin sakinsa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: