Ma’aikatan jiragen sama a Najeriya sun yi barazanar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani muddin ba a cika musu burinsu ba.

Sakataren ƙungiyar ƙwararrun matuƙa jirgin sama Kwamared Abdulsaq Saidu ne ya shaida haka ya na mai tabbatar da cewar a shirye su ke domin dakatar da duk wata harkar sufurin jirgin sama a Najeriya.

Gamayyar ma’aikatan ce ta dauki matakin tsunduma yajin aikin bayan shafe shekara da shekaru ba a biyasu alawus alawus da wasu alƙawura da gwamnatin ta ƙi cikawa.

Duk da cewar gwamnatin tarayya ta buƙaci zama dasu tare da buƙatar janye yajin aikin gargaɗi dasu ka yi, sai dai sun koka a kan cewar ba a zauna dasu ba balle jin buƙatun dasu ke ɗauke dasu.

Ma’aikatan filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Abuja, sun yi yajin aikin gargaɗi tare da zanga-zanga a ranar Talata.

Sannan sun bai wa gwamnatin mako guda don ganin ta sauraresu tare da cika musu burin su ko kuwa su tafi yajin aikin daga dukkan tashoshin jiragen sama na faɗin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: