- Shugaban ruundunar sojin RSF na kasar Sudan da ta kwashe makonni na rikici Muhammed Hammed Hamdan Dagalo ya bayyana cewa a shirye yake da a a tattauna da shi domin wanzar da zaman lafiya.
Hammed ya bayyana hakanne ga jaridar BBC ta wayar tarho ya ce a shirye ya ke da ya tattauna da bangaren da suke rikici da juna amma bayan an tsagaita wuta.

Cikin tattaunawar ya ce ba ya son a lalata sudan amma zai iya karbar yarejeniyar tsagaita wuta bayan an daina jefa nakiya.
Hammed ya ce yana zargin manyan hafsoshin sojin sudan kamar Abbel Fattah da Burhan da nufin tayar da zaune tsaye.

Sai dai shi ma janar Burhan ya ce zai amince da tattaunawar ido da ido tare dukkan wadanda ake rikicin da su.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka samu yarjejeniyar tsagaita wuta bayan da kasashen duniya su ka shiga rikacin ta fuskar difilomasiyya da kuma majalissar dinkin duniya.
Sai dai babban hafsan Hammed ya ce ba shi da wata matsala da Burhan amma yana masa kallon maci amana.
Yakin sudan wanda aka shafe makonni ana yi sakamakon rikici akan mulki ya jawo asarar rayuka da kuma barnar dukiya ma tarin yawa.