An tsinci gawarwakin wasu mutane biyu a daren ranar Litinin lokacin da wasu da ake zaton yan bindiga ne suka farmaki yankin Kofar Kona da ke garin Zariya, jihar Kaduna.

Majiyoyi sun bayyana cewa tsagerun yan bindigar dauke da makami sun isa yankin ne a kafa da misalin karfe 9:40 na dare sannan suka garzaya gidan wani jami’in hukumar kwastam.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaye sunansa ya ce, Yan bindigar wadanda suka zo su da yawa sun farmaki gidan wani jami’in kwastam, Malam Abubakar Modibbo sannan suka yi garkuwa da matarsa Asiya Abubakar da yaranta mata su biyu, Khadijatul Kubra da Hafsat, da kuma wani Falalu Ibrahim.

Wani dan kungiyar yan sa kai ya ce yan bindigar wadanda suka gaggauta garzayawa kauyen Dorayi a wajen garin Zariya sun yi fashin shanu.

A cewarsa, sun kuma sace mutane da dama kimanin su 20.
Ya ce yan bindigar sun yi watsi da dukkanin mutanen da suka sace a yankin sannan suka tsere zuwa jeji, bayan musayar wuta da jami’an tsaro.
Duk wani kokari na jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ya ci tura don wayoyinsa sun ki shiga, har zuwa lokacin da mu ke kawo muku wannan labarin.