Wasu mutane mazauna Kaduna a arewacin Najeriya sun nuna damuwa a kan yadda su ke ganin baƙin fuska da ake zargi yan bindiga ne.

 

Ana zargin mutanen da aikata ta’addanci tare da guduwa wasu yankuna na Kaduna domin neman mafaka.

 

Mutanen da ake zargi na samun matsin lamba daga jihar Zamfara kuma su ke tserewa zuwa wasu kauyuka a Kaduna.

 

Mutane a garin Damari da ke karamar hukumar Birnin Gwari a Kaduna sun ce yan bindiga na ta zaarya a kauykan da rana tsaka.

 

Sannan mutanen na yin barazanar garkuwa da manoma a yankin.

 

Tun a ranar Talata yan bindigan su ka fara shiga dajin Kuduru kaakar yadda wani Saeed ya bayyanawa wakilin jaridar Daily Trust.

 

Jihar Kaduna ta sh afama da hare-haren yan bindiga tun baayan kammala babban zabe a Najeriya.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: