Babban bakin Najeriya CBN ya ce kwanaki 30 ne su ka rage masa domin rufe dukkan asusun da ba su da lambobin tantancewa na BVN.

Tun tuni babban bankin y bayar da umarni ga bankunan kasuwanci da su tabbatar sun haɗa lambobin asusun ajiyar kwastomominsu da BVN.

A wani bayani da bankin ya tattara a ranar 8 Afrilun da ya gabata babban bankin ya ce mutane miliyan 57.39 su ka haɗa asusun ajiyar bankinsu da BVN.

Bankin ya samar da tsarin ne domin daƙile ayyukan masu aikata damfara, da kuma gane ƙididdigar adadin mutanen da ke da asusun ajiya na banki a ƙasar.

Tsarin da bankin ya fitar ya ce babu wani asusun ajiya na banki da zi ci gaba da aiki nan da kwnaki 30 matuƙar ba a haɗashi da lambobin tantancewa na BVN ba.

Akwai matakai da dama da masu asusun ajiyar da aka rufe musu za su bi kafin asusun ajiyar ya koma aiki musamman ma asusun ajiyar kamfanoni, da makamantansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: