NoSakataren gwamnatin kasar Amurka, Antony Blinken ya tabbatar da cewa za su yi aiki da zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu domin karfafa alaka.

A wani jawabi da zababben shugaban Najeriya ya fitar, jaridar Vanguard ta ce Asiwaju Bola Tinubu ya tabbatar da cewa sun yi waya da Antony Blinken a ranar Talata.
Tunde Rahman ya ce Sakataren na gwamnatin Shugaba Joe Biden ya shafe tsawon mintuna 20 yana zantawa da mai gidansa ta wayar salula a jiya.

A yayin tattaunawarsu ya shaidawa shugaba mai jiran gado za su hada-kai da shi domin taimakawa kasashen.

Jawabin da Tunde Rahman ya fitar, ya ce Bola Tinubu ya yi alkawarin zai kama aiki gadan-gadan da zarar an rantsar da shi a karshen wata.
Haka zalika, Tinubu ya sha alwashi gwamnatinsa da za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayun 2023 za tayi kokari wajen samun alaka mai kyau da Amurka.