Sanata mai wakilta Borno ta kudu Sanata Mahammad Aliyu Ndume ya bayyana cewa indai gwamnatin tarayyar Najeriiya ta ciyo bashin dala miliyan 800 zai kai ta kotu.

Sanata Aliyu Ndume ya bayyana haka ne a jiya a wata hira da aka yi da shi a babban birnin tarayyar Abuja.
Gwamnatin Najeriiya ta bayyana cewa za ta ciyo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya domin rage radadin cire tallafiin man fetur da gwamnatin za ta cire wanda ta aike da kudirin ga majalissar dattawan a farkon watan Afrilun da ya gabata.

kuma Gwamnati ta ce idan aka karbo bashin za a rabawa alummnar kasar ne mutum miliyan 50 da kuma rabawa magidanta.

Sannan kamar yadda bankin duniyar ya bayyana ya ce zai bai wa Najeriiya bashi da zarar ta nema.
Sai dai ana tsaka da haka sai aka jiyo dan majalissar Ndume yana mai cewa shi kuwa indai gwamnati ta ciyo bashi zai kai ta kara gaban kotun domin abun ba zai yiwa kasa dadi ba.
Dan haka indai aka ciyo bashin zai jefa kasar a wani hali kuma hakan ya sabawa dokar.
Ya ci gaba da cewa akalla kudaden da za a ciyo bashin dala miliiyan 800 ba zai isa a rabawa mutane miliyan 50 ba.
Kuma ko da za a raba musu kuudaden zai kama ne naira 7,200 kaga kuwa wannan ba za su amfanar ba kawai dai ana so ne a bai wa wasu su cinye kudaden kamar yadda BBC ta ruwaito.