Kungiyar kare musulmi ta kasa Najeriiya wato MURIC ta bayyana cewa ta na goyon bayan kirista ya kasance shugaban majalissar Dattijai ta goma a kasar.

Shugaban kungiyar MURIC na kasa Farfesa Ishak Akiintola shi ne ya bayyana haka a cikin wata tattaunawarsa da yan jaridu.
Ya ce sakamakon sa toka sa katsi da aka dinga yi a lookacin da ake neman tikitin shugabancin kasa Najeriya .

ya ce hakan ya nuna akwai damuwa iindai aka bari musulmi ya zama shugaban majalissar Dattijai ta kasa da za a yi karo na Goma.

ya ci gaba da cewa tunda dai kasa Najeriya ta samu shugaban kasa musulmi tare da mataimakinsa to dole ya zama shugaban majallissar ya zama kirista kuma daga bangaren kudu.
Akintola ya ce indai ana so kasar ta samu zaman lafiya to ya kamata a samu kirista ya zama shugaban.
Daga karshe kungiyar musulmi MURIC ta ce duk musulmin da ya ke neman takarar su janyewa yan takara daga Kudu saboda kasa ta samu dai daiton musulmi da kirista a kasa baki daya kamar yadda yake ya bayyana.