Gwamnatin Jihar Sokoto ta karrama Wasu Manyan Malamai da shugabanni ‘yan Asalin Jihar.

Sanarwar hakan na zuwa ne ta hannun kwamishinan Shari’a na Jihar Sulaiman Usman SAN a yayin da ya ke jawabi a gurin taron majalisar Zartarwa na Jihar.

Gwamatin ta sanar da sauya sunan Jami’ar Jihar SSU zuwa sunan Sheikh Abdullah I Fodiyo wanda ya kasance kani ga Sheikh Usmanu Dan Fodiyo.

Sannan itama Jami’ar Ilmi ta Jihar SSUE an sauya mata sunan Tsohon shugaban Kasar Najeriya Alhaji Shehu Shagari.

Gwamnatin ta kuma sanya sunan Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari SSCOE zuwa Sunan Marigayi Sultan Ibrahim Dasuki.

Gwamnatin ta sake karrama Ambasada Shehu Malami Sarkin Sudan din Wurno kuma tsohon babban kwamishinan Najeriya a Kasar Afrika ta Kudu ,inda aka sanya sunansa a Kwalejin Noma da Kiwon Dabbobi CAAS da ke Wurno.

Sanarwar ta kara da cewa an sake sauya Susan Kwalejin Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci ta Wamakko CLIS zuwa Sunan Sheikh Halliru Binji College Of Law and Islamic Studies, yayin da ita kuma Kwalejin koyon aikin Jinya ta Tambuwal aka sauya Mata suna zuwa Balaraba Buda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: