Rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra ta samu nasarar ceto mutane biyu daga cikin mutane Bakwai da aka yi garkuwa da su a lokacin da aka Kai’wa tawagar ma’aikatan ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya da ke Jihar.

 

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Ikenga Tochukwu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

 

Ikenga ya ce mutanen da aka kubtar an kubtar da su ne ba tare da wata jikkata ba.

 

Sanarwar ta kara da cewa jami’an na ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin domin samun cikakken bayani.

 

‘Yan bimdigan Sun yi garkuwa da mutanen a ranar Talata a lokacin da su ka yi musu kwantan bauna ciki harda ma’aikata uku a ciki daga bisani su ka kone

motocin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: