Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika roko ga majalissar dattawan Najeriya don maidawa jihar Borno naira Biliyan 16.

Cikin rokon shugaban Muhammadu Buhari da ya mikawa majalisar yana mai neman majalissar ta sahalemasa ya mayarwa da gwamnatin jihar Borno kudade kimanin naira biliyan 16 domin baiwa gwamnatin Zulum.
Takardar da shugaban majalissar dattawan kasar Ahmada Lawan ya karanta a yau Talata ya ce Buhari ya na neman majalissar ta yarjemasa ya fidda kudin.

Kudaden sune wadanda aka yi amfani wajen ayukan tituna da asibitoci da dai sauransu.
