Kwanaki shida su ka rage wa shugaba Buhari ya sauka daga kargar mulki yana so ya cika dukkanin alkawarin ya daukawa mutanen kasar.
Kasa na Najeriya ta fado izuwa kasa ta biyu a cikin jerin kasashen da ke da arzikin man fetur a Afrika.

Kasar ta Najeriya dai ta kasance ta biyu wadda ke da arzikin man fetur a kasashen Afrika wadda ke bayan kasar Angola a yanzu haka.

Kuma kamar yadda masana ke bayani sun ce abin da ya sanya Najeriya ta yi baya a jerin, sakamakon masu satar danyen mai da kuma fasa bututun man sanadin rashin tsaro.

Ajiya Litinin ne dai shugaban kasa Mahammadu Buhari ya kaddamar da babbar matatar man fetur ta DanGote wadda ake ganin za ta kawowa Najeriya ci gaba a bangaren abubuwan da suka shafi man fetur.

Wani masani a bangaren da ya shafi harkar man fetur Dakta Ahmad ya bayyana cewa matatar DanGote za ta amfanar da kasa Najeriya matukar anbi wasu matakai.

Ya ce matakan sune dole a samarwa da sabuwar matatar danyen man da zai dinga isar ta.

Dukda ya ce ko yanzu haka kasa Najeriiya ba ta ya iya samarwa da kanta danyen man da zai ishi matatar.

Amma hakan ya faru ne sakamakon fasa bututun man da kuma satarsa da ake yi a yanzu haka.

Ya ci gaba da cewa indai Najeriya ba ta samarwa matatar ba to dole ne ta samowa kanta danyen man da za ta yi amfani da shi, kuma yin haka zai sanya fetur ya kara tsada a Najeriya.

An dai kiyasta kasa Najeriya nada gangar danyen man fetur a kwance a kasa kimanin Ganga Biliyan 16 zuwa 22 duk da ana kara samun wasu karin daga cikin rijiyoyin man.

Leave a Reply

%d bloggers like this: