Mai Alfamar sarkin Musulmi Muhammad Sa’adu Abubakar lll ya musanta maganar da ake yi akansa cewa, jami’an tsaro sukan kauce domin yan bindiga su kai hari.

Sarkin ya bayyana haka ne a wani taro da aka yi da kungiyar addinai wanda sakataren kungiyar Farfesa Crnelius Afebu Omonokhuwa.
Sarkin ya ce bai san maganar cewa jami’an tsaro suna kaucewa domin akai wa yan bindiga hari ba.

Ya ce yan bindiga su kan shiga kauyuka tare da hallakan mutane su kona dukiyarsu a yayin da aka kammala, sai jami’ai su je domin kwantar da tarzoma.

Sarkin musulmi Sa’adu na lll ya ce wannan maganar bai santa ba kuma bai san an yi ba.