Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa cutar Amai da gudawa ta barke a kasashen Afrika 15.

Cikin kasashen da suke da cutar akwai muzammique, Congo, Estwani, Kenya, da kuma Afrika ta kudu.
Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana haka ne inda ta ce cutar Amai da gudawa ta hallaka akalla mutane 15 a kasar Afrika ta kudu tare da kama wasu mutane.

kuma ta kama mutane a kasar Afrika ta kudu yayin da ake kara tsoron kamuwar wasu.

Sannan hukumar ta ce kasar malawi ke kan gaba a yawan masu kamuwa da cutar ta Amai da gudawa.
Sai dai kasar Afrika ta kudu ta bayyana cewa an dauki mataki game da lamarin hadi da iyakokin kasar da ta yadda za a magance matsalar