Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayyana wata tawaga ta mutane Tara wadda za ta jagoranci rantsuwar sabon shugaban kasa Ahmad Bola Tunubu a ranar 29 5 2023.

Cikin wata sanarwa daga fadar gwamnatin ta Amurka ta fitar a jiya Litinin.
Cikin sanarawar da aka fitar daga fadar ta Amurka ta ce shugaban kasar Joe Biden ya ce zai tura tawaga ta mutane Tara don halartar bikin rantsuwar zababben shugaban Najeriya Boa Ahmed Tunubu.

A ranar 29 ga watan Mayu ne dai ake saran za a rantsar da sabon shugaban kasa Bola Ahmad Tunubu bayan lashe zabe da yayi.

Taron wanda za a gudanar a babban filin Eagle Squre dake babban birnin tarayyar Abuja.
kuma tun a ranar 27 ga wata tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta zai fara gudanar da makala akan hadin kan kasashen don habaka tsarin damakwaradiyya.