Hukumar kare fararen hulu ta kasa Najeriya NSCDC reshen jihar kano ta tabbatar da kama wasu matasa Biyar da ake zargin masu kwacen waya.

Da yake jawabi mai magana da yawun hukumar ta NSCDC Ibrahim Abdullahi ya bayyana haka ga yan jaridu yau Alhamis.

Ibrahim ya ce jami’an sun kama wadanda ake zargin har mutum biyar a ranar Talata 23 ga wata mayu 2023.

Ya ce kamen sun yi shi ne ranar Talata a unguwar Sabon Gari karamar hukumar Fagge ta kano.

Akwai wasu karin mutane biyu da ake zargin masu siyan wayar sata ne.

Kuma an baza jamiai don kamo sauran mutane biyu don tabbatar musu da doka.

Kakakin ya ci gaba da cewa hukumar NSCDC za ta dakile harkar kwacen waya a kano
kuma duk mai shirin aikata wani mugun aiki yayi shirin dainawa don kuwa ba zai tsira ba .

Leave a Reply

%d bloggers like this: