
Manoman kaji a jihar Kano sun koka bias yadda ake kokarin rabasu da sana arsu ta karfin tsiya.
Shugaban masu kiwonkaji a jihar Kano Umar Kibiya ne ya bayyaa hakan yayin zantarwarsa da mujallar Matashiya.

Ya ce mambobin ƙungiyar da su ka haura mutum 6,000 na cikin wani hali duba ga ana kawo wani kwai da basu yarda da ingancinsa ba ake siyarwa da al ummar Kano wanda zai iya gurɓata musu lafiya kasancewar bas u yarda da ingancinsa ba.

Ya ce a cikin mutane 6,000 kowanne akwai sama da mutum ɗari a ƙarƙashinsa.
A nasu bangaren, masu kiwon kaji a jihar Kano sun bayyana cewar ana kawo kwai mota mota daga wata jihar kuma hakan na neman rabasu da sana arsu.
Muhammad Aminu Adamu wanda yayi Magana a madadin masu kiwon kaji na Kano ya shaida mana cewar, akwai bukatar gwamnatin jihar ano ta sa ido duba ga cewar za a tara matasan da basu da aikin yi a jihar.
kusan mutane miliyan daya manoman kaji ne za su rasa aikinsu ba tare da gwamnati ta Ankara ba.