Sabon shugaban gidan rediyo Kano Hon Hisham Habib ya sha alwashin magance matsalolin da gidan rediyon ya ke fuskanta.

Hisham Habib wanda Gwaamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya nadashi a matsayin shugaban gidan ya fara aiki a yau Litinin.

A yayin jawabin da ya yi wa maaikatan gidan jim kadan bayna shigarsa a yau, ya ce zai tabbata

magance matsalolin tare da aiki da ma’aikata domin ciyar da gidan gaba.

Hisham Habib ya yi aiki a manyan jaridun Najeriya tare da aiki a ma’aikatar yada labarai ta jihar.

A nasa jawabin shugaban ƙungiyar yan jarida a Kano Comrade Abbas Ibrahim ya ce wannna ba abin mamaki bane domin an ajiye kwarya a gurbinta ganin yadda sabon shugaban yake jajirtacce kuma dan jarida da yayi gwagqarmayar aikin kuma yake cikin kungiyar.

Sannan ya ce a shirye su ke da su bayar da shawara ganin yadda ya shafe sama da shekaru 30 a matsayin maaikacin gidan rediyo Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: