Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya NAFDAC ta ce za ta fara kamawa tare da gurfanar da masu tallan magunguna a kan titi.

Babbar daarakta a hukumar Mojisola Adeyeye ce ta baayyana haka a wani taron don fito da illar tallan maginguna a tituna wanda ya gudana yau a Abuja.


Sannan ta umarci jami’an hukumar da su tabbata sun ƙara shiri wajen kula tare da kamawa sannna a gurfanar da duk wanda aka samu yaana taallan magungunan a titi.
Ta ce daƙile tallan magungunan naa daga cikin kudirinta wandaa ta ce za su haɗa kia da kafofin yada labarai wajen magance matsalar ta hanyar wayar da kai.
A jawaabinta ta ce hakan na ciwa mutane tuwo a kwarya ganin yadda ma’aikatu da dama ke nuna damuwa a kai.
Sannan ta ce za su tabbata sun maagance yadda wasu ke amfani da wasu sinadarai wajen nunar da kayaan marmari waand ata ce hakan na da illa ga fatar jiki.
Sannan taa ce amfani da sinadaran na iya haifar da ciwon koda da kuma wasu cutukan.