Hukumar yi wa ƙasa hidima NYSC ta sauya sansaninta a jihar Filato.

Biyo bayan cigaba da samun hare-hare da ke silar rasa rayuwaar jama’a wanda hakaan ya sany a gwamnati a jihar ta sanya dokar hana fita a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar.


A wata sanarwa da mai magan ada yawun yan saandan jihar DSP Alabo Alfred ya fitar, ya ce kwamishinan yan sandan jihar ya kai ziyara zuwa sansanin masu hidimar ƙasar na wucin gadi.
Ziyarar da kwamishinan ya kai, sun yi ne domin haɗa kai don inganta tsaro da samar da cigaba a ɓangaren.
Hukumar ta samu matsuguni na wucin gadi a Waaya Foundation da ke Dei Du a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu.
Ko a ranar Lahadi sai da ƙungiyar Fulani makiyaya su ka ce an hallaka mutane da damaa tare da kone gidajensu.
Sannan sun rasa dabbobinsu da makiyayan ke kiwo sama da dubu biyu.
Karamar Hukumar Mangu na fama da hare-hare da ke salwantar da rayuka da dukiyoyin al’umma.