Rundunar sojin Najeriya ta kone wani jirgin ruwa da ake zargi mallaki masu satar danyen mai ne.

An cinna wuta a jirgin a yankin Escravos a Naija Delta.

Jirgin da aka kama n akna hanyarsa ta zuwa ƙasar Kamaru wanda ke dauke da danyen mai mai yawa.

Tun a ranar Litinin kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce ya sanar da kama jirgin da aka yi.

Ana zargin an sato danyen man daga jihar Delta da kuma ya kai lita 800,000.

Jirgin mallakin wani kamfani ne a Najeriya wanda ya shafe shekara 12 yana aikin satar man a cewar hukumomin.

Sai dai ba su bayyana ko an kwashe danyen man kafin kone jirgin ba.

Ana fama da satar danyen mai da fasa bututu wanda a Najeriya hakan ke fama da matsalar tattalin arzikin ƙasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: