Gwamnatin kasar Faransa za ta fara bayar da wani kuɗi ga al’ummar ƙasar domin gyara tufafi da takalmansu.

Gwamnatin za ta fara bayar da kuɗin daga watan Oktoba mai kamawa.
Hakan ya fito daga bakin karamar sakatariyar muhalli Berangere Couillard ranar Talata a birnin Paris.

An ɗauki matakin hakan ne da nufin hana zubar da tsaffin tufafi aa ƙasar.

Cikin shekara guda gwamnatin ta ce an zubar da tufafi da nauyinsu ya kai tan 700,000.
Gwamnatin ta buƙaci masu gyara da sarrafa takalma da masu ɗinkin da su shiga ciki don cin gajiyar tsarin.
Akwai kayan sakawa da takalma biliyan 3.3 wanda aka kai kasuwa a shekarar 2022, kamar yadda masu sabuntawa su ka tabbatar.
Ƙarƙashin tsarin kwastomomi za su sami tallafin yuro 7.7 daga cikin yuro miliyan 154 da aka samar ƙarƙashin tsarin.