Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar tsaron farin kaya da ta tuhumi Godwin Emefiele dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya a kotu cikin mako ɗaya ko kuma ta sallameshi.

Kotun ta ba da wannan umarni ne a lokacin sauraron ƙarar da Emefiele ya shigar don tabbatar da ‘yancinsa na ɗan’adam, inda yake ƙalubalantar kamawa da tsare shi da Hukumar DSS tayi a

ranar Asabar 10 ga watan Yuni ne Hukumar DSS ta ba da sanarwar cewa ta kama tare da tsare, Godwin Emefiele.

Da farko dai hukumar ta DSS ta ce Emefiele ba ya hannunta, kafin daga bisani ta tabbatar da cewa da kamashi.

Tun a daren Juma’a ne, wasu rahotanni suka

ce jami’an tsaro sun yi awon gaba da shi, jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da shi daga kan muƙaminsa.

“DSS na tabbatar da cewa Emefiele, dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, yanzu haka yana hannunta don gudanar da bincike,” a cewar wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu da jam’iyyarsa ta APC sun zargi Emefiele da yunƙurin hana su cin zaɓen da aka kammala cikin watan Fabrairu saboda tsarin rage kuɗi a hannun jama’a da ya ƙaddamar da kuma canza fasalin naira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: