Hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta bayyana cewa ta gurfanar da dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele a gaban kotu.

Gurfanarwar na zuwa ne bayan umarnin da wata Babbar Kotu a birnin tarayya Abuja ta bayar a ranar Alhamis.

Kotun ta bai’wa jami’an na DSS umarnin cewa ta gurfanar da Emefiele cikin mako daya ko kuma ta sallameshi.

DSS ta gurfanar da Emefiele ne Sa’o’i kadan baya umarnin da kotun ta bayar wanda hakan ya sanya mai magana da yawun hukumar Peter Afunanya ya sanar da bayar da umarnin gurfanar dashi domin yin biyayya ga umarnin kotun.

DSS ta gurfanar da Emefiele ne a ranar Juma’a 9 ga watan Yunin da ya gabata bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar dashi daga kan mukaminsa na Gwamnan Babban Bankin ƙasa.

Bayan dakatar dashi kuma hukumar ta DSS ta kamashi.

Amma har kawo yanzu ba a bayyana tuhume-tuhume da ake yiwa dakataccen gwamnan babban bankin ba a gaban kotun.

Kafin gurfanar da Emefiele a gaban Kotun babban lauya a Najeriya mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam Femi Falana SAN ya shawarci hukumar ta DSS da ta bar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gurfanar da Emefiele a gaban kotun sakamakon zarginsa da ake yi da yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa.

Falana ya bayyana cewa kamata ya yi da zarar hukumar ta DSS ta kammala bincike akansa ta aike dashi zuwa ga hukumar ta EFCC domin gurfanar dashi a gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: