Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na III ya ayyana ranar Laraba a matsayin daya ga sabuwar shekarar musulunci ta 1445 wadda ta yi daidai da 19 ga watan Yulin 2023.

Sarkin wanda ya bayar da umarnin fara duban watan tun a ranar Litinin, inda ya ce al’ummar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Al Muharram na sabuwar shekarar ta Musulunci.
Watan Almuharram shi ne wanda ya kasance watan farko a tsarin kalandar musulunci ta hijirar Annabi Muhammad S,AW daga garin Makka zuwa Madina.

Majalisar Sarkin Musulmi ta cikin sanarwar da ta fitar ta ce sakamakon rashin ganin jinjirin wata a faɗin Najeriya a ranar Litinin ne ya sanya Laraba ta kasance 1 daya ga sabuwar shekarar 1445.

