Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a Bola Ahmed Tinubu ya nemi amincewar majalisar dokokin Najeriya don aike da dakarun sojin ƙasar zuwa Nijar don karɓe ikon mulki daga hannun soji.

Wasiƙar da shugaban ya aikewa majalisar wanda ya ayyana matsayar ƙungiyar ECOWAS ya nemi sahalewarsu dangane da matakin da ƙungiyar ta ɗauka.

Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya karanta wasiƙar wanda ya ce ƙungiyar ECOWAS na yin takaicin yadda aka hamɓarar da mulkin demokaraɗiyya a ƙasar Nijar.

Sannan akwai matakai da ƙungiyar ta ɗauka dangane da matsayar da aka cimma wajen aike da dakarun soji wanda ƙungioyar ta ce za a yi amfani da kafofin sada zumunta wajen wayar da kan mutane a dangane da matakin.

Kuma za a rufe dukkanin iyakokin Najeriya da Nijar na sama da ƙasa da kuma hana shigar da kaya daga Najeriya zuwa Nijar.
Haka kuma za a katse harkokin sufuri na ƙasa da sama daga shiga Nijar ko shigowa Najeriya daga Nijar.

Wasiƙar ta ce za a rufe hanyoyin shigar da kaya daga jihar Legas tare da tabbatar da bin dukkanin tsarin da aka yi a kai.

Idan ba a manta ba sojin Najeriya sun shaidawa ƙungiyar ECOWAS cewa babu wani zaɓi da ya rage illa amfani da ƙarfin soji don ƙwace mulkin daga hannun sojin Nijar tare da mayar da shi zuwa farar hula.

Leave a Reply

%d bloggers like this: