Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na nuni da cewar an tashi baram-baram tsakanin kwamitin sasanci da wakilan juyin mulkin soji na ƙasar.

Tawagar ECOWAS ta aike da ƙwaƙƙwaran kwamiti domin sasantawa ta yadda za a mayar da mulki hannun farar hula a ruwan sanyi.

Shugaban ƙungiyar ECOWAS Bola Ahmed Tinubu ya aike da kwamiti mai ƙarfi a ranar Alhamis domin tattaunawa da wakilan sojin da su ka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar.

Sai dai zaman bai haifar da ɗa mai ido ba.
Wakilcin wanda Janar Abdussalam Abubakar mai ritaya ya jagoranta, tare da ganawa da wakilan juyin mulkin ƙasar.

Ƙasar Nijar ta ƙi amincewa da sasanci bayan da ƙasashen Togo, Faransa da kuma ƙasar Amuruka.

Gidan Rediyo France Intanational ya ruwaito cewar an yi watsi da zaman sasanci da ƙasashen su ka yi ba tare da an cimma wata matsaya a kai ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: